Hausa translation of the meaning Page No 208

Quran in Hausa Language - Page no 208 208

Suratul Yunus from 1 to 6


Sũratu Yũnus
Tanã karantar da tauhĩdin Ubangiji game da jan hankali zuwa ga abũbuwan halitta waɗanda suka shãfi mutãne wajen amfãni da su.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. A. L̃. R. Waɗancan ãyõyin littãfi ne kyautatacce.
2. Shin, yã zama abin mãmaki ga mutãne dõmin Mun yi wahayi zuwa ga wani namiji daga gare su cẽwa, « Ka yi gargaɗi ga mutãne kuma ka yi bushãra ga waɗanda suka yi ĩmãni da cẽwa: Lalle ne sunã da abin gabãtarwar gaskiya a wurin Ubangijinsu. » Kãfirai suka ce: « Lalle ne wannan, haƙĩƙa, masihirci ne bayyananne. »
3. Lalle Allah ne Ubangijinku wanda Ya halicci sammai da ƙasa a cikin kwãna shida, sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi Yanã gudãnar da al'amari. Bãbu wani macẽci fãce a bayan izninSa. Wannan ne Allah, Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Shin fa, ba ku tunãni?
4. zuwa gare Shi makõmarku take gabã ɗaya, wa'adin Allah gaskiya ne. Haƙĩƙa, Shi ne Yake fara halitta, sa'an nan kuma Ya mayar da ita dõmin Ya sãka wa waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai da ãdalci, kuma waɗanda suka kãfirta sunã da abin sha daga ruwan zãfi, da azãba mai raɗaɗi, sabõda abin da suka kasance sunã yi na kãfirci.
5. Shĩ ne wanda Ya sanya muku rãnã, babban haske, da watã mai haske, kuma Ya ƙaddara shi ga Manzilõli, dõmin ku san ƙidãyar shẽkaru da lissãfi. Allah bai halitta wannan ba, fãce da gaskiya, Yanã bayyana ãyõyi daki- daki dõmin mutãne waɗanda suke sani.
6. Lalle ne a cikin sãɓãwar dare da yini, da abin da Allah Ya halitta a cikin sammai da ƙasa, haƙĩƙaakwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin taƙawa.