Hausa translation of the meaning Page No 249

Quran in Hausa Language - Page no 249 249

Suratul Al-Ra'd from 1 to 5


Sũratur Ra‘ad
Tanã karantar da tauhĩdi, bisa jan hankali ga dũba zuwa ga ayõyin halitta, da bayãnin kiran Allah zuwa ga mutãne, da tabbatar da Manzancin Annabi Muhammadu, a cikin magana mai zurfi ga hankali.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. A. L̃. M̃. R. Waɗancan ayõyin littãfi ne kuma abin da aka saukar gare ka daga Ubangijinka ne gaskiya, kuma amma mafi yawan mutãne bã su yin ĩmãni.
2. Allah Shi ne wanda Ya ɗaukaka sammai, bã da ginshiƙai ba waɗanda kuke ganin su. Sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi, kuma Ya hõre rãnã da watã, kõwane yanã gudãna zuwa ga ajali ambatacce. Yanã shirya al'amari, Yanã rarrabe ãyõyi daki- daki, mai yiwuwa ne ku yi yaƙĩni da haɗuwa da Ubangijinku.
3. Kuma shĩ, ne wanda Ya shimfiɗa kasa, kuma Ya sanya duwãtsu da kõguna a cikinta, kuma daga dukan 'ya'yan itãce Ya sanya ma'aura biyu cikinsu. Yanã sanya dare ya rufe yini. Lalle ne a cikin wancan, haƙĩƙa akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin tunãni.
4. Kuma a cikin ƙasa akwai yankuna mãsu maƙwabtaka, da gõnaki na inabõbi da shũka da dabĩnai iri guda, da waɗanda bã iri guda ba, anã shayar da su da ruwa guda. Kuma Munã fĩfĩta sãshensa a kan sãshe a wajen ci. Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga muiãne waɗanda suke hankalta.
5. Kuma idan ka yi mãmãki, to, mãmãkin kam shi ne maganarsu, « Shin, idan muka kasance turɓãya, zã mu zama a cikin wata halitta sãbuwa? » Waɗancan ne waɗanda suka kãfirta da Ubangijinsu, kuma waɗanda akwai ƙuƙumai a cikin wuyõyinsu, kuma waɗancan ne abõkan wuta. Sũ, a cikinta, mãsu dawwama ne.