Hausa translation of the meaning Page No 282

Quran in Hausa Language - Page no 282 282

Suratul Al-Asra from 1 to 7


Sũratul Isrã’
Tanã karantar da daidaitãwa a tsãkãnin abũbuwa mãSu dangantaka da jũnã.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Tsarki ya tabbata ga wanda Ya yi tafiyar dare ( 1 ) da bãwanSa da dare daga Masallaci mai alfarma zuwa ga Masallaci mafi nĩsa ( 2 ) wanda Muka sanya albarka a gefensa dõmin Mu nũna masa daga ãyõyinMu. Lalle ne Shi shĩ ne Mai ji, Mai gani.
2. Kuma Mun bai wa Mũsã ( 3 ) littafi, kuma Mun sanya shi shiriya ga Banĩ Isrã'ila, cẽwa kada ku riƙi wani wakĩli baiciNa.
3. Zuriyar waɗanda Muka ɗauka tãre da Nũhu. Lalle ne shi ya kasance wani bãwa mai gõdiya.
4. Kuma Mun hukunta zuwa ga Bani Isrã'ĩla a cikin Littãfi, cewa lalle ne, kunã yin ɓarna a cikin ƙasa sau biyu, kuma lalle ne kunã zãlunci, zãlunci mai girma.
5. To idan wa'adin na farkonsu yajẽ, za Mu aika, a kanku waɗansu bãyi ( 4 ) Nãmu, ma'abũta yãƙi mafĩ tsanani, har su yi yãwo a tsakãnin gidãjenku, kuma yã zama wa'adi abin aikatawa.
6. Sa'an nan kuma Mu nwayar da ɗauki a gare ku a kansu, kuma Mu taimake ku da dũkiyõyi da ɗiya kuma Mu sanya ku mafiya yawan mãsu fita yãƙi.
7. Idan kun kyautata, kun kyautata dõmin kanku, kuma idan kun mũnana to dõmĩnsu. Sa'an nan idan wa'adin na ƙarshe ( 5 ) ya jẽ, ( za su je ) dõmin su baƙanta fuskokinku, kuma su shiga masallaci kamar yadda suka shige shi a farkon lõkaci, kuma dõmin su halakar da abin da suka rinjaya a kansa, halakarwa.
( 1 ) Isrã'i, shi ne tafiyar dare daAllah Ya yi da Annabi daga Makka zuwa Baitil Maƙadis. Sa'an nan Mi'iraji zuwa sama inda aka ba shi sallõli.
( 2 ) Muƙarana a tsakãnin Masjidil Harãm watau tsararre daga a yãki mutãnensa da MasjidilAƙsã wanda ba tsararre ba. Isrã'i da Mi'irãji sun fi Miƙãtin Mũsã da gãnãwarsa da Ubangiji a Ɗũr- Sĩna'a.
( 3 ) Tsakãnin Bãwan Allah Muhammadu da Mũsã, kuma an aiko Mũsãga Banĩ Isrã'ila kawai, kuma Nũhu an ce masa bãwa amma ba a jingina shi kamar yadda aka jingina bawanSa ba. Sa'an nan kuma Jingina Yahũdu ga Nũhu ya daidaita su da sauran mutãne wajen da'awar ɗaukaka da nasaba.
( 4 ) Sun yi fasãdi da barin aiki da Taurãti, sabõda haka aka aika Jãlũta a kansu. Ya kashe su kuma ya kãma zuriyarsu.
( 5 ) Suka yi fasãdi marra ta biyuda kashe zakariyya da Yahaya, sai aka aika musu da Bukht Nasar daga Bãbila ya karkashe su, kuma ya kãma zuriyarsu, kuma ya rũshe Baitil Maƙadis. Waɗannan lãbaru biyu na ɓarnar Banĩ Isrã'ila sunã cikin bãyar da lãbaru ga gaibi. Idan an daidaita su da lãbarun gaibi waɗanda Alƙur'ãni ya faɗã, waɗansu suka auku kuma waɗansu sunã ta aukuwa zã a san falalar Alƙur'ãni a kan Taurãti kamar yadda ya bayyana cẽwa Attaura ta yi kira zuwa ga tauhidi da shiriya, sa'an nan ya bayyana abũbuwan da Alƙur'ãnĩ yake karantarwa daga ãyã ta 9 zuwa ga ãyã ta 38 inda ya tãra hãlãyen ƙwarai kuma ya kõre mũnãna.