Hausa translation of the meaning Page No 332

Quran in Hausa Language - Page no 332 332

Suratul Al-Hajj from 1 to 5


Sũratul Ḥajj
Tanã karantar da yadda ake tsarkake aƙĩda daga al’ãdu, kuma a tsare ta daga gare su, kada a cũɗanya ta da su.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Yã ku mutãne! Ku bi Ubangijinku da taƙawa. Lalle ne girgizar ( 1 ) ƙasa ta tsayuwar Sa'a wata aba ce mai girma.
2. A rãnar da kuke ganin ta dukan mai shãyar da mãma tanã shagala daga abin da ta shãyar, kuma dukan mai ciki tanã haihuwar cikinta, kuma kanã ganin mutãne sunã mãsu mãyẽ alhãli kuwa su bã mãsu mãye ba, amma azãbar Allah ce mai tsanani.
3. Akwai daga mutãne ( 2 ) wanda yake yin musũ ga sha'anin Allah bã da wani ilmi ba, kuma yanã biyar kõwane Shaiɗan mai taurin kai.
4. An wajabta masa cẽwa wanda ya jiɓince shi, to, lalle ne sai ya ɓatar da shi, kuma ya shiryar da shi zuwa ga azãbar sa'ĩr.
5. Ya ku mutãne! Idan kun kasance a cikin shakka a Tãshin Ƙiyãma, to, lalle ne Mũ, Man halittaku daga turɓaya, sa'an nan kuma daga gudãjin jini, sa'an nan kuma daga taõka wadda ake halittãwa da wadda ba a halittawa dõmin, Mu bayyana muku. Kuma Munã tab batar da abin da Muke so a cikin mahaifa zuwa ga wani ajali ambatacce, sa'an nan kuma Munã fitar da ku kunã jãrĩri, sa'an nan kuma dõmin ku kai ga cikar ƙarfinku. Kuma daga cikin ku akwai wanda ke mutuwa, kuma daga gare ku akwai wanda ake mayarwa zuwa ga mafi ƙasƙancin rãyuwa dõmin kada ya san kõme a bãyan ya sani. Kuma kanã ganin ƙasa shiru, sa'an nan idan Muka saukar da ruwa a kanta, sai ta girgiza kuma ta kumbura, kuma ta tsirar da tsirrai daga kõwane nau'i mai ban sha'awa.
( 1 ) Addĩni tsantsa shĩ ne ke sanya ƙafa ta tsaya da kyau. Idan an cũɗanya addĩni da wasu abũbuwa na bidi'a kõ al'ãdu, to, ƙafa bã ta iya tsayi balle ma a lõkacin girgizar ƙasã ta tsayin Sa'a.
( 2 ) An raba mutãne a game da addĩni kashi huɗu, sa'annan ya fãra da kashi na farko mafi yawa daga cikin sauran kasũsuwan, watau kashin wãwãye mãsu biyar Shaiɗan ga al'ãdu da son zũciyõyi su bar hukunce- hakuncen Allah.