Hausa translation of the meaning Page No 453

Quran in Hausa Language - Page no 453 453

Suratul Sad from 1 to 16


Sũratu Ṣ
Tanã karantar da hanyar mulkin Musulunci da yadda ake gudãnar da sharĩ’a da ãdalci, da gargaɗi ga bin wata hanya.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Ṣ̃, Inã rantsuwa da Al- ƙur'ãni mai hukunce- hukunce.
2. Ã'a, waɗanda suka kãfirta sunã cikin girman kai ( ga rikon al'ãdunsu ) da sãɓãni ( tsakãnin jũnansu ) .
3. Da yawa Muka halakar da wani ƙarni, a gabãninsu, suka yi kira ( nẽman cẽto ) , bãbu lõkacin kuɓucewa.
4. Kuma suka yi mãmãki dõmin Mai gargaɗi, daga cikinsu, ya je musu. Kuma kãfirai sukace, « Wannan mai sihiri ne, maƙaryaci. »
5. « Shin, yã sanya gumãka duka su zama abin bautawa guda? Lalle wannan, haƙĩƙa, abu ne mai ban mãmaki! »
6. Shũgabanni daga cikinsu, suka tafi ( suka ce ) , « Ku yi tafiyarku, ku yi haƙuri a kan abũbuwan bautawarku. Lalle wannan, haƙiƙa, wani abu ne ake nufi! »
7. « Ba mu taɓa ji ba, game da wannan a cikin addinin ƙarshe. Wannan bai zama ba fãce ƙiren ƙarya. »
8. « Shin, an saukar da Alƙur'ãni ne a kansa, a tsakãninmu ( mũ kuma ba mu gani ba ) ? » Ã'a, su dai sunã cikin shakka daga hukunciNa Ã'a, ba su i da ɗanɗanar azãba ba.
9. Ko kuma a wurinsu ne ake ajiye taskõkin rahamar Ubangijinka, Mabuwãyi, Mai yawan kyauta?
10. Kõ kuma sũ ne da mallakar sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu? To sai su hau a cikin sammai ( dõmin, su hana saukar Alƙur'ãni ga Muhammadu ) .
11. Rundunõni ne abin da ke can, rusassu, na ƙungiyõyinsu.
12. Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, da Ãdãwa da Fir'auna mai turãkun ( da suka kafe mulkinsa ) .
13. Da Samũdãwa da mutãnen Luɗu da ma'abũta ƙunci, ( 1 ) waɗancan ne ƙungiyõyin.
14. Bãbu kõwa a cikinsu fãce ya ƙaryata Manzanni, sabõda haka azãbãTa ta wajaba.
15. Kuma waɗannan ( 2 ) bã su jiran kõme fãce tsãwã guda, wadda bã ta da hani.
16. Kuma suka ce: « Ya Ubangijinmu! Ka gaggauta mana da rabonmu, a gabãnin rãnar bincike. » ( 3 )
( 1 ) Mutãnen ƙunci, sũ ne mutãnen Annabi Shu'aibu. A cikin Sham suke.
( 2 ) Watau mutãnen Annabi Muhammadu: Ƙuraishãwa da waninsu har ya zuwa Tashin Ƙiyãma.
( 3 ) Wannan ita ce maganar dukan kãfirai na kõwane zãmani mãsu nẽman rabon dũniya kawai, ba su yarda da Tãshin Ƙiyãma ba, balle sãmun sakamako a cikinsa.