Hausa translation of the meaning Page No 489

Quran in Hausa Language - Page no 489 489

Suratul Al-Shura from 52 to 10


52. Kuma kamar wancan Mun aika wani rũhi ( rai mai haɗa jama'a ) zuwa gare ka, daga gare Mu. Ba ka kasance kã san abin da yake littãfi ba, kõ abin da Yake ĩmãni, kuma amma Mun sanya shi ( rũhin, watau Alƙur'ãni ) wani haske ne, Munã shiryar da wanda Muke so daga cikin bãyĩnMu game da shi. Kuma Lalle kai, haƙĩƙa, kanã shiryarwa zuwa ga hanya, madaidaiciya.
53. Hanyar Allah wanda ke da mulkin abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa. To, zuwa ga Allah kawai al'amura ke kõmãwa.
Sũratuz Zukhruf
Tanã karantar da hãlãyen mutãne na son riƙon al’adunsu da jayayya da ƙarya dõmin haka a kan gaSkiya.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Ḥ. M̃.
2. Ina rantsuwa da Littãfi Mabayyani.
3. Lalle Mũ, Mun sanya shi abin karãtu na Lãrabci, tsammãninku, kunã hankalta.
4. Kuma lalle, shĩ, a cikin uwar littãfi a wurin Mu, haƙĩƙa, maɗaukaki ne, bayyananne.
5. Shin, zã Mu kau da kai daga saukar da hukunci daga gare ku ne dõmin kun kasance mutane mãsu ɓarna?
6. Alhãli kuwa sau nawa Muka ( 1 ) aika wani Annabi a cikin mutãnen fãrko!
7. Kuma wani Annabi bai je musu ba fãce sun kasance, game da shi, sunã mãsu yin izgili.
8. Sai Muka halakar da waɗanda suke sũ ne mafiya ƙarfin damƙa daga gare su. Kuma abin misãlin mutãnen farkon ya shũɗe.
9. Kuma lalle ne, idan ka tambaye su, « Wãne ne ya halitta sammai da ƙasa? » Lalle zã su ce, « Mabuwãyi Mai ilmi ne Ya halitta su. »
10. Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa kuma Ya sanya muku hanyõyi a cikinta, tsammãninku za ku nẽmi shiryuwa.'
( 1 ) Tun da ba Mu bar mutãnen farko mãsu ɓarna ba, sai da Muka aika musu Manzanni, kuma kõwace ƙungiya daga cikin waɗanda aka aika wawani Manzo sai da ta yi izgili game da Manzonsu, har abin ya kai ga halakar shũgabanninsu. To, haka mutãnenka, bã zã Mu bar su ba, sabõda ɓarnansu, sai Mun aike kazuwa gare su, su yi izgili game da kai, har a halaka shũgabanninsu, sa'an nan sauransu, su bi abin da aka umurce su da shi.