Hausa translation of the meaning Page No 50

Quran in Hausa Language - Page no 50 50

Suratul Al-Imran from 1 to 9


Sũratu Ãl ‘Imrana
Tanã karantar da cẽwa Allah yana karɓa addu’ar wanda ya kira Shi da gaskiyar niyya, kuma yana keta al’ãdu da wannan kira.Bãbu abin da yake da wuya ga Allah idan an kaɗaita Shi da tsarkakẽwa daga shirki da abin da ya yi kama da shirki.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. A. L̃.M̃.
2. Allah, bãbu wani abin bautawa fãce Shi, Rãyayye Mai tsayuwa da kõme.
3. Yã sassaukar da Littãfi a gare ka da gaskiya, yana mai gaskatãwa ga abin da ke gaba gare shi, kuma Allah Yã saukar da Attaura da Linjĩlã.
4. A gabãni, suna shiryar da mutãne, kuma Ya saukar da littattafai mãsu rarrabẽwa. Lalle ne waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Allah, suna da azãba mai tsanani. Kuma Allah Mabuwayi ne, Ma'abucin azãbar rãmuwa.
5. Lalle ne, Allah bãbu wani abin da ke ɓõyuwa gare Shi a cikin ƙasa, kuma bãbu a cikin sama.
6. Shi ne wanda Yake suranta ku a cikin mahaifu yadda Yake so. Bãbu abin bautãwa fãce Shi Mabuwãyi, Mai hikima.
7. Shi ne wanda ya saukar da Littãfi a gare ka, daga cikinsa akwai ãyõyi bayyanannu, su ne mafi yawan Littãfin, da wasu mãsu kamã da jũna. To, amma waɗanda yake a cikin zukãtansu akwai karkata sai suna bin abin da yake da kamã da jũna daga gare shi, dõmin nẽman yin fitina da tãwĩlinsa. Kuma bãbu wanda ya san tãwĩlinsafãce Allah. Kuma matabbata a cikin ilmi sunã cẽwa: « Mun yi ĩmãni da Shi; dukkansa daga wurin Ubangijinmu yake. » Kuma bãbu mai tunãni fãce ma'abũta hankula.
8. Yã Ubangijinmu! Kada Ka karkatar da zukãtanmu bãyan har Kã shiryar da mu, kuma Ka bã mu rahama daga gunKa. Lalle ne, Kai, Kai ne Mai yawan kyauta.
9. « Yã Ubangijimu! Lalle ne Kai, Mai tãra mutãne ne dõmin wani yini wanda bãbu shakka a gare shi, Lalle ne Allah bã Ya sãɓãwar lõkacin alkawari. »