Hausa translation of the meaning Page No 502

Quran in Hausa Language - Page no 502 502

Suratul Al-Jathiya from 33 to 5


33. Kuma mũnanan abin da suka aikata ya bayyana a gare su, kuma abin da suka kasance sunã yi na izgili ya wajaba a kansu.
34. Kuma aka ce: « A yau zã Mu manta da ku, kamar yadda kuka manta da gamuwa da yininku wannan. Kuma mãkõmarku wutã ce, Kuma bã ku da waɗansu mãsu taimako. »
35. « Wancan dõmin lalle kũ, kun riƙi ãyõyin Allah da izgili, Kuma rãyuwar dũniya ta rũɗe ku. To, a yau bã zã su fita daga gare ta ba, Kuma bã zã su zama waɗanda ake nẽman yardarsu ba. »
36. Sabõda haka, gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin sammai, kuma Ubangijin ƙasã, Ubangijin halittu.
37. Kuma gare Shi girma yake, a cikin sammai da ƙasã, kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai Hikima.
Sũratul Aḥƙãf
Tanã karantar da cẽwa duka mai yin nasĩha ga kansa, ko ga wani, to, mai gargaɗi ne, Annabi ne kõ waninsa, mutum ne kõ aljani.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Ḥ. M̃.
2. Saukar da littafi daga Allah, Mabuwãyi, Mai hikima yake.
3. Ba Mu halitta sammai da ƙasa ba, da abin da ke tsakãninsu, fãce da gaskiya da wani ajali ambatacce, kuma waɗanda suka kãfirta, mãsu bijirẽwa ne daga abin da aka yi musu gargaɗi ( da shi ) .
4. Ka ce: « Shin, kun gani, abin da kuke kira, wanda yake baicin Allah? Ku nũna mini, menene suka halitta daga ƙasa? Kõ kuwa sunã da tãrayya a cikin sammai? Ku zo mini da wani littãfi na gabãnin wannan ( Alƙur'ãni ) kõ wata alãma daga wani ilmi, idan kun kasance mãsu gaskiya. »
5. Kuma wãne ne mafi ɓata daga wanda ke kiran wanin Allah wanda da bã zai karɓa masa ba, bar Rãnar Kyama, alhãli sũ ( waɗanda ake kiran ) shagaltattu ne daga kiransu?