Hausa translation of the meaning Page No 515

Quran in Hausa Language - Page no 515 515

Suratul Al-Fath from 29 to 4


29. Muhammadu Manron Allah ne. Kuma waɗannan da ke tãre da shi mãsu tsanani ne a kan kãfirai, mãsu rahama ne a tsakãninsu, kanã ganin su sunã mãsu rukũ'i mãsu sujada, sunã nẽman falala ( 1 ) daga Ubangijinsu, da yardarSa. Alãmarsu tanã a cikin fuskõkinsu, daga kufan sujuda. ( 2 ) Wannan shĩ ne siffarsu a cikin Attaura. Kuma siffarsu,a cikin Injĩla ita ce kamar tsiron shũka wanda ya fitar da rẽshensa, sa'an nan ya ƙarfafa shi, ya yi kauri, sa'an nan ya daidaita a kan ƙafãfunsa, yanã bãyar da sha'awa ga mãsu shũkar' dõmin ( Allah ) Ya fusãtar da kãfirai game da su. Kuma Allah Ya yi wa'adi ga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, daga cikinsu, da gãfara da ijãra mai girma.
Sũratul Ḥujurãt
Tanã karantar da hãlãyen ƙwarai da ladubba na addini da na zaman jama’a a tsakãninsu.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku gabãta ( da kõme ) gaba ga Allah da ManzonSa. ( 3 ) Kuma ku yi ɗã'ã ga Allah da taƙawa. Lalle Allah Mai ji ne, Masani.
2. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku ɗaukaka saututtukanku ( 4 ) bisa sautin Annabi, kuma kada ku bayyana sauti gare shi a magana, kamar bayyanãwar sãshenku ga sãshe, dõmin kada ayyukanku su ɓãci, alhãli kuwa kũ ba ku sani ba.
3. Lalle waɗanda ke runtsẽwar saututtukansu a wurin Manzon Allah waɗannan ne waɗanda Allah Yã, jarrabi zukãtansu ga taƙawa. Sunã da wata irin gãfara da ijãra mai girma.
4. Lalle waɗanda ke kiranka daga bãyan ɗakuna, mafi Yawansu bã su aiki da hankali.
( 1 ) Nẽman falala da sana'ar hannunsu, kõ fatauci, ba su zama nauyi a kan mutãne ba, kõwanensu ya dõgara ga Allah,sa'an nan yanã rãyuwa a kan hãlãliyarsa.
( 2 ) Kufan sujuda, shĩ ne hasken fuskõkinsu da annurinsu. fuska ita ce madũbin zũciya. Anã gãne zũciyar ƙwarai daga fuskarta. Bã ya halatta ga mutumya riƙa darkãka gõshinsa ga ƙasã dõmin ya yi kwãdon salla. Wannan alãmar riya ce. Faɗakarwa. Nan ne ƙarshen dõgãyen sũrõri da ake cẽ wa Muɗawwalãtu. An ƙãresu da sũrõri biyu, Ƙitãl dõmin yãƙi, da fat'h dõmin tsãrin gudãnar da siyãsa sabõda tsaron Addĩni. Bãyan haka kuma sai gajẽrun sũrõri, watau Mufassalãtu.
( 3 ) Wannan yã nũna mana cẽwabã yã halatta ga Musulmi ya yi wani aiki ko ya faɗi wata magana sai yã san hukuncin Allah a cikinsu. Kuma kada ya ƙãra wãyõnsa a kan abinda Allah Yã ce, kuma kada ya rage idan yanã da ĩkon cikãwa. Dukan wannan yakan ja Musulmi ga ɓãcin ayyukansa, watau ya yi ridda daga Musulunci.
( 4 ) Ladubban zama da shugaba.Annabi shi ne kan shugabanni, sai dai ɗã'a gare shi wãjibi ne ga kõme, sauran shũgabanni kuwa ga abin da bai sãɓa wa shari'a ba.