Hausa translation of the meaning Page No 531

Quran in Hausa Language - Page no 531 531

Suratul Al-Qamar from 50 to 16


50. Kuma umurninMu bai zamo ba fãce da kalma ɗaya, kamar walƙãwar ido.
51. Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun halaka irin gayyarku. To, shin, akwai mai tunãni?
52. Kuma kõwane abu, da suka aikata shi, yanã a cikin littattafai.
53. Kuma dukkan ƙarami da babba, rubutacce ne.
54. Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna da kõguna.
55. A cikin mazaunin gaskiya, wurin Mai ikon yi, Mai iya zartaswa.
Sũratur Raḥmãn
Tana karantar da ni’imõmin Allah nau’inau’i ga mutãne da aljannu a dũniya da Lãhira, kuma tanã kwaɗaitar da su ga gõde wa Allah Mai ni’imtar da su.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. ( Allah ) Mai rahama.
2. Yã sanar da Alƙur'ani.
3. Yã halitta mutum.
4. Yã sanar da shi bayãni ( magana ) .
5. Rãnã da watã a kan lissãfi suke.
6. Kuma tsirrai mãsu yãɗo da itãce sunã tawãlu'i.
7. Kuma samã Ya ɗaukaka ta, Kuma Yã aza sikẽli.
8. Dõmin kada ku karkatar da sikẽlin.
9. Kuma ku daidaita awo da ãdalci, kuma kada ku rage sikẽlin.
10. Kuma ƙasã Yã aza ta dõmin tãlikai.
11. A cikinta akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno mai kwasfa.
12. Da ƙwãya mai sõshiya da ƙamshi.
13. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangjinku ( 1 ) kuke ƙaryatãwa?
14. Yã halitta mutum daga ƙẽkasasshen yumɓu kumar kasko.
15. Kuma ya halitta aljani daga bira daga wutã.
16. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
( 1 ) Asalin lamiri « ku » yanã nũni ne ga nau'i biyu, watau mutãne da aljannu, sai dai bãbu lamirin abu biyu kawai a cikin Hausa, sai na jama'a. Jam'i a luggar Hausa ya fara daga biyu.