Hausa translation of the meaning Page No 553

Quran in Hausa Language - Page no 553 553

Suratul Al-Jumu'ah from 1 to 8


Sũratul Jum‘ah
Tanã karantar da cẽwa ɗaukar ilmi bã da yin aiki da shi ba, bã shi da wani amfãni sai wahalar banza.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin kasã sunã tasbĩhi ga Allah, Mamallaki,Mai tsarki' Mabuwãyi, Mai hikima.
2. Shĩ ne wanda Ya aika, a cikin mabiya al'ãdu, ( 1 ) wani Manzo daga gare su yanã karanta ãyõyinSa a kansu, kuma yanã tsarkake su, kuma yanã sanar da su littafin da hikimarsa kõ da yake sun kasance daga gabãninsa lalle sunã a cikin ɓata bayyanãnna.
3. Da waɗansu mutãne ( 2 ) daga gare su, ba su i da riskuwa da sũ ba, alhãli kuwa shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.
4. Waccan wata falalar Allah ce Yanã bãyar da ita ga wanda Yake so. Kuma Allah ne Ma'abũcin dukan falala mai girma.
5. Misãlin waɗanda aka ɗõra wa ɗaukar Attaura sa'an nan ba su ɗauke ta ba, kamar misãlin jãki ne Yanã ɗaukar littattafai. Tir da misãlin mutãnen ( 3 ) nan da suka ƙaryatã game da ãyõyin Allah! Kuma Allah bã Yã shiryar da mutãnẽ azzãlumai.
6. Ka ce: « Yã kũ waɗandasuka tũba ( Yahũdu ) ! Idan kun riya cẽwa kũ ne zãɓaɓɓun Allah bã sauran mutanẽ ba, sai ku yi gũrin mutuwa ( 4 ) idan kun kasance mãsu gaskiya. »
7. Kuma bã zã su yi gũrinta ba har abadã sabõda abin da hannãyen su suka gabãtar. Kuma Allah ne masani ga azzãlumai
8. Ka ce « Lalle mutuwar nan da kuke gudũ daga gareta,to, lalle ita mai haɗuwa da ku ce sa'an nan kuma anã mayar da kũ zuwa ga masanin fake da bayyane, dõmin Ya bãku lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa. »
( 1 ) Lãrabawa sũ ne mabiya al'ãdu, watau ummiyyũn daga ummu, watau uwa watau kamar yadda uwãye suka haife su dõmin bã su da wani littãfi da suke bi sai al'ãdonsu da hukunce- hukuncen shaihunansu.
( 2 ) Su ne Ajamãwan da zã su musulunta su bi Annabi tsira da aminicin Allah su tabbata a gare shi. Kõ kuwa duk wandaya musulunta a bãyan sahabban Annabi. Wannan yanã nunã falalar sahabbai a kan waɗansunsu.
( 3 ) Tir da wanda ya yi siffa da irin siffõfin Yahũdu daga Musulmi wajen ɗaukar karãtun Alƙur'ãni amma kuma bai yi aiki da shi ba. Yahaya bn Yamãni ya ce: « Sunã rubuta nadĩsi bã su fahimtarsa, kuma bã su kula da ma' anarsa. » Watau sunã wahala wajen ɗaukar ilmin da aka ɗõra musu ɗaukarsa amma kuma bã su yin amfãni da shi a wajen aikinsu da mu'ãmalõlinsu.
( 4 ) Ba a sãduwa da Allah sai a bãyan mutuwa. Masõyi nã gũrin sãduwa da masõyinsa, kuma bã zai yi gudun sababin sãduwar ba.