Hausa translation of the meaning Page No 591

Quran in Hausa Language - Page no 591 591

Suratul Al-Tariq from 1 to 15


Sũratut Ɗãriƙ
Tana karantar da tsaron Al1ah ga kome bisa ga tsari, kuma kome asĩrinsa ne, Alƙur’ãni gaskiya ne da asirĩ, Allah Yã tsare Shi daga mai son ya ɓãta shi.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Inã rantsuwa da sama da mai aukõwa da dare.
2. To, mẽ yã sanar da kai abin da ake cẽwa mai aukõwa da dare?
3. Shi ne taurãron nan mai tsananin haske. ( 1 )
4. Bãbu wani rai fãce a kansa akwai wani mai tsaro.
5. To, mutum ya dũba, daga mẽ aka halittã shi?
6. An halittã shi daga wani ruwa mai tunkuɗar jũna.
7. Yanã fita daga tsakanin tsatso da karankarman ƙirji.
8. Lalle ne Shi ( Allah ) , ga mayar da shi ( mutum ) , tabbas Mai iyãwa ne.
9. Rãnar da ake jarrabawar asirai.
10. Saboda haka, bã shi da wani ƙarfi, kuma bã shi da wani mai taimako ( da zai iya kãre shi daga azãbar Allah ) .
11. Ina rantsuwa da sama ma'abũciyar ruwa mai kõmãwa yana yankẽwa.
12. Da ƙasa ma'abũciyar tsãgẽwa, ( 2 )
13. Lalle ne shĩ ( Alƙur'ãni ) , haƙĩƙa magana ce daki- daki ( 3 )
14. Kuma shĩ bã bananci ( 4 ) bane
15. Lalle ne sũ, suna ƙulla kaidi na sõsai.
16. Kuma Ni, Ina mayar da kaidi ( gare su ) kamar yadda suke ƙulla kaidi.
17. Saboda haka, ka yi wa kafirai jinkiri, ka dakata musu, sannu- sannu.
Sũratul A‘ala
Tana karantar da cewa rãyarwa da matarwa ga hannun Allahsuke, sũ kuma nau’i- nau’i ne.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mafi ɗaukaka.
2. Wanda Yã yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar.
3. Kuma Wanda Ya ƙaddara ( abin da Ya so ) sannan Ya shiryar, ( da mutum ga hanyar alhẽri da ta sharri ) .
4. Kuma Wanda Ya fitar da makiyãyã.
5. Sa'an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa.
6. Za mu karantar da kai ( Alƙur'ãni ) sabõda haka bã zã ka mantã ( shi ) ba.
7. Fãce abin da Allah Ya so, lalle ne Shi ( Allah ) Ya san bayyane da abin da yake bõye.
8. Kuma za Mu sauƙaƙe maka ( al'amari ) zuwa ga ( Shari'a ) mai sauƙi.
9. Sabõda baka, ka tunãtar, idan tunatarwa zã ta yi amfãni.
10. Wanda yake tsõron ( Allah ) Zai tuna.
11. Kuma shaƙiyyi, zai nisanceta,
12. Wanda zai shiga wutar da tã fi girma.
13. Sa'an nan bã zai mutu ba a cikinta, kuma bã zai rãyu ba.
14. Lalle ne wanda ya tsarkaka ( da ĩmãni ) yã sãmu babban rabo.
15. Kuma ya ambaci sũnan ( 5 ) Ubangijinsa, sa'an nan yã yi salla.
( 1 ) Wannan ya yi kama da zuwan Annabi a cikin jahiliyya don ya haskaka duniya da ilimi kamar yadda girgije ke ba da ruwa saboda tsiron ƙasa, hantsar uwa ta ba da nono saboda jariri kuma maniyi ya zo lokacin Jima'i.
( 2 ) Dõmin fitar tsiro.
( 3 ) Mai rabewa tsakanin ƙarya da gaskiya.
( 4 ) Kãkãci.
( 5 ) Ya ambaci sũnan Allah ga ayyukansa duka, ya yi sallolin nan biyar da sauran.