Hausa translation of the meaning Page No 594

Quran in Hausa Language - Page no 594 594

Suratul Al-Fajr from 24 to 20


24. Yana dinga cẽwa, « Kaitona, dã na gabatar ( da aikin ƙwarai ) domin rãyuwata! »
25. To, a rãnar nan bãbu wani mai yin azãba irin azãbar Allah.
26. Kuma bãbu wani mai ɗauri irin ɗaurinSa.
27. Yã kai rai mai natsuwa!
28. Ka koma zuwa ga Ubangijinka, alhãli kana mai yarda ( da abin da Ya ƙaddara maka a dũniya ) abar yardarwa ( da sakamakon da zã a ba ka a Lãhira ) .
29. Sabõbda haka, ka shiga cikin bãyiNa ( mãsu bin umurui a dũniya ) .
30. Kuma ka shiga AljannaTa ( a Lãhira ) .
Sũratul Balad
Tana karantar da cewa mutum an halitta shi cikin wahala, komai amfanin sa idan ya bi umurnin Allah ko kuwa mai cũtar sa idan ya saɓa wa umurnin Allah.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Bã sai Na yi rantsuwa da wannan gari ( 1 ) ba.
2. Alhãli kai kanã mai sauka a cikin wannan gari.
3. Da mahaifi da abin da ya haifa.
4. Lalle ne, Mun halitta mutum cikin wahala.
5. Kõ yanã zaton bãbu wani mai iya sãmun iko, a kansa?
6. Yana cẽwa « Na ( 2 ) halakarda dũkiya mai yawa, »
7. Shin, yana zaton cewa wani bai gan shi ba?
8. Shin, ba Mu sanya masa idãnu biyu ba?
9. Da harshe, da leɓɓa biyu.
10. Kuma ba Mu shiryar da shi ga hanyõyi ( 3 ) biyu ba?
11. To, don mene ne bai shiga Aƙabã ba?
12. Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cẽ wa Aƙabã?
13. Ita ce fansar wuyan bãwa.
14. Ko kuwa ciyarwa, a cikin yini ma'abũcin yunwa.
15. Ga marãya ma'abũcin zumunta.
16. Ko kuwa wani matalauci ma'abũcin turɓãya.
17. Sa'an nan kuma ya kasance daga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi wa jũna wasiyya da yin haƙuri, kuma suka yi wa jũna wasiyya da tausayi.
18. Waɗannan ne ma'abũta albarka ( 4 )
19. Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyinMu, sũ ne ma'abũta shu'umci ( 5 )
20. A kansu akwai wata wuta abar kullewa.
( 1 ) Allah Ya ce ba sai Ya yi rantsuwa da Makka ba, sa'an nan zã a san darajarta a lõkacinda Annabi yake a cikinta, kuma shi yana da haƙƙin zama a cikinta mahaifansa da zurriyarsa duka, ko da yake zai yi hijira sabõda fitinar kãfirai mãsu halaka dũkiyarsu kanadãwa da shi. Dã sun yi amfãni da dukiyar ga ayyukan alhẽri, dã yã fi musu.
( 2 ) Nã halaka dukiya mai yawa dõmin faɗã da addĩni.
( 3 ) Hanyar alhẽri da ta sharri.
( 4 ) Ko kuwa waɗanda ake bai wa takardunsu ga dãma, a Lãhira.
( 5 ) Ko kuwa waɗanda ake bai wa takardunsu ga hagu, a Lãhira.