Hausa translation of the meaning Page No 596

Quran in Hausa Language - Page no 596 596

Suratul Al-Lail from 15 to 8


15. Bãbu mai shigarta sai mafi shaƙãwa.
16. Wanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya.
17. Kuma mafi taƙawa ( 1 ) zai nisance ta.
18. Wanda yake bãyar da dũkiyarsa ,alhãli yana tsarkaka.
19. Alhãli bãbu wani mai wata ni'ima wurinsa wadda ake nẽman sakamakonta.
20. Fãce dai nẽman yardar Ubangijinsa Mafi ɗaukaka.
21. To, lalle ne zai yarda ( da sakamakon da zã a bã shi ) .
Sũratuḍ Ḍuḥã
Tana karantar da ni’imõmin da Allah Yã yi wa Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a game da zãtinSa, dõmin Ya gina wasu hukunce- hukunce a kansu.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Inã rantsuwa da hantsi.
2. Da dare a lõkacin da ya rufe ( da duhunsa ) .
3. Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba.
4. Kuma lalle ta ƙarshe ( 2 ) ce mafi alheri a gare ka daga ta farko.
5. Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta bã ka kyauta sai ka yarda.
6. Ashe, bai sãme ka marãya ba, sa'an nan Ya yi maka makõma?
7. Kuma Ya sãme ka bã ka da shari'ã, sai Ya shiryar da kai?
8. Kuma Ya sãme ka matalauci, sai Ya wadãtã ka?
9. Sabõda haka, amma marãya, to, kada ka rinjãye shi.
10. Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa tsãwa.
11. Kuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka faɗa ( dõmin gõdiya ) .
Sũratush Sharh
Tana karantar da ni’imõmin da Allah Ya yi wa Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, game da sifõfinsa, dõmin Ya gina wasu hukunce- hukunce a kansu.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Ba Mu bũɗa maka zũciyarka ba ( dõmin ɗaukar haƙuri da fahimta ) ?
2. Kuma Muka saryar maka da nauyinka, Ashe.
3. Wanda ya nauyayi bãyanka?
4. Kuma Muka ɗaukaka maka ambatonka?
5. To, lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.
6. Lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.
7. Sabõda haka idan ka ƙãre ( ibãda ) sai ka kafu ( kana rõƙon Allah ) .
8. Kuma zuwa ga Ubangijinka ka yi kwaɗayi.
( 1 ) Mafi taƙawa da Mafi shaƙãwa suna ma'anar mai taƙawa da shaƙiyyi.
( 2 ) Ta ƙarshe, wãto, Lãhira; kuma ta farko, wato, dũniya.