Hausa translation of the meaning Page No 601

Quran in Hausa Language - Page no 601 601

Suratul Al-'Asr from 1 to 5


Sũratul ‘Aṣr
Tana bayãnin cẽwa kõme mutum ya yi a lõkacinsa hasãra ne da ɓarnar zarafi, sai fa idan ibãda ce yake yi.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Ina rantsuwa da zãmani. ( 1 )
2. Lalle ne mutum yana a cikin hasara.
3. Fãce waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka yi wa juna wasiyya da bin gaskiya, kuma suka yi wa juna wasiyya da yin haƙuri ( su kam, basu cikin hasara ) .
Sũratul Humaza
Tana bayãni ga hana aibanta wasu mutãne, da hana gulma da raɗa a tsakãnin Musulmi dõmin ginin al’umma ya tabbata, wanda ya karya shi, a sanya shi wuta ta cikin ginin shikã- shikai.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Bone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunɗe ( mai raɗa ) .
2. Wanda ya tara dũkiya, kuma ya mayar da ita abar tattalinsa.
3. Yana zaton cẽwa dũkiyarsa za ta dawwamar da shi.
4. A'aha! Lalle ne zã a jẽfa shi a cikin Huɗama.
5. Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa Huɗama?
6. Wutar Allah ce wadda ake hurawa.
7. Wadda take lẽƙãwa a kan zukata.
8. Lalle ne ita abar kullẽwa cea kansu.
9. A cikin wasu ginshiƙai mĩƙaƙƙu.
Sũratul Fĩl
Tana nũna darajar Hurumin Makkah, yadda Allah Yake halakar da mai nufinta da yãƙi ko wani sharri.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Ashe, ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata ga mutanen giwa ( 2 ) ba?
2. Ashe, bai sanya kaidinsu a cikin ɓata ba?
3. Kuma Ya sako, a kansu, wasu tsuntsãye, jama'a- jama'a.
4. Suna jifar su da wasu duwatsu na yumɓun wuta.
5. Sa'an nan Ya sanya su kamar karmami wanda aka cinye?
( 1 ) Wasu suna fassarawa da lokacin sallar La'asar da kuma marece. A kõwane dai, an bai wa lokaci muhimmanci, zãmani yana yanke wanda baiyanke shi ba. ba ya halatta ga mutum wata mudda ta zãmani ta wuce shi bai san amfãnin da ya sãma wa kansa a cikinta ba, kuma kõme ya sãmu idan ba addini ba ne, to, hasãrace.
( 2 ) An yi Yãƙin Gĩwa shẽkarar haifuwar Annabi tsakãnin halaka su da haifuwarsa kwãna hamsin. Bayan shekara arba'in Annabi ya fara karantar da mutane. Ya karantar da su cikin shekara ashirin da uku, sa'an nan ya ƙaura. Bayansa da shekara hamsin waanda suka bi shi suka cinye duniya. Wannan yana nuna cewa mutane ba su samun daraja sai da riƙon addini da ilimi.