Hausa translation of the meaning Page No 604

Quran in Hausa Language - Page no 604 604

Suratul Al-Ikhlas from 1 to 6


Sũratul Ikhlãṣ
Tana karantar da tauhidi, watau kaɗaita Allah wanda ke areaddininSa daga maƙiyansa.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Ka ce: « Shi ne Allah Makaɗaĩci. »
2. « Allah wanda ake nufin Sa da buƙata. »
3. « Bai haifa ba, kuma ba a haife Shi ba. »
4. « Kuma babu ɗaya da ya kasance tamka a gare Shi. »
Sũratul Falaƙ
Tana karantar da yadda ake nẽman tsarin Allah daga sharri duka, daga maƙiyi na bayyane.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Ka ce « ina neman tsari ga Ubangijin safiya »
2. « Daga sharrin abin da Ya halitta. »
3. « Da sharrin dare, idan ya yi duhu. »
4. « Da sharrin mãtã mãsu tõfi a cikin ƙulle- ƙulle. »
5. « Da sharrin mai hãsada idan ya yi hasada. »
Sũratun Nãs
Tana karantar da yadda ake nẽman tsari daga sharrin shaiɗan na mutum da na aljani.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Ka ce « Ina nẽman tsari ga Ubangijin mutãne. »
2. « Mamallakin mutane. »
3. « Abin bautãwar mutãne. »
4. « Daga sharrin mai sanya wasuwãsi, mai ɓoyewa. » ( 1 )
5. « Wanda ke sanya wasuwãsi a cikin ƙirãzan mutane. »
6. « Daga aljannu da mutane. »
( 1 ) Shaiɗan yakan ɓõye idan ya ji an ambaci sunan Allah, dõmin haka aka yi masa suna mai ɓõyewa, wãto bã ya zuma wurin da ake karatu dawa'azi, kamar yadda bã ya zama cikin zũciyar mutum mai ibãda da gaskiya. Ibãda ta gaskiya ita ce wadda aka yi ta kamar yadda Allah Ya ce a yi ta. Banda ibãdar bidi'a, ba ta korar Shaiɗan. Kuma da sharaɗin a yi ibãdar da kyakkyawar niyya, dõmin aikin da bãbu niyya mai kyãwo game da shi ɓãtacce ne.