Hausa translation of the meaning Page No 251

Quran in Hausa Language - Page no 251 251

Suratul Al-Ra'd from 14 to 18


14. Yanã da kiran gaskiya, kuma waɗanda ( kãfirai ) suke kira baicinsa, bã su karɓa musu da kõme fãce kamar mai shimfiɗa tãfukansa Zuwa ga ruwa ( na girgije ) dõmin ( ruwan ) ya kai ga bãkinsa, kuma shi bã mai kaiwa gare shi ba. Kuma kiran kãfirai ( ga wanin Allah ) bai zama ( 1 ) ba fãce yanã a cikin ɓata.
15. Kuma sabõda Allah wanda yake a cikin sammai da ƙasa suke yin sujada, so da ƙi, kuma da inuwõyinsu, a sãfe da maraice.
16. Ka ce: « Wãne ne Ubangijin sammai da ƙasa? » Ka ce: « Allah » . Ka ce: « Ashe fa, kun riƙi waɗansu masõya baicin Shi, waɗanda ba su mallaka wa kansu wani amfãni ba kuma haka bã su tũre wata cũta? » Ka ce: « Shin makãho da mai gani sunã daidaita? Kõ shin duhu da haske sunã daidaita? ko sun sanya ga Allah waɗansu abõkan tãrayya waɗanda suka yi halitta kamar halittarSa sa'an nan halittar ta yi kama da jũna a gare su? » Ka ce: « Allah ne Mai halitta kõme kuma Shĩ ne Maɗaukaki, Marinjãyi. »
17. Ya saukar da ruwa daga sama ( 2 ) , sai magudanai suka gudãna da gwargwadonsu, Sa'an nan kõgi ya ɗauki kumfa mai ƙãruwa, kuma daga abin da suke zuga a kansa ( azurfa ko zinari kõ ƙarfe ) a cikin wuta dõmin nẽman ado kõ kuwa kãyan ɗãki akwai kumfa misãlinsa ( kumfar ruwa ) . Kamar wancan ne Allah Yake bayyana gaskiya da ƙarya. To, amma kumfa, sai ya tafi ƙẽƙasasshe, kumaamma abin da yake amfãnin mutãne sai ya zauna a cikin ƙasa. Kamar wancan ne Allah Yake bayyana misãlai.
18. Ga waɗanda ( 3 ) suka karɓa wa Ubangijinsu akwai abu mafi kyau a gare su, kuma waɗanda suke ba su karɓa Masa ba, to, lalle dã sunã da abin da yake a cikin ƙasa gaba ɗaya da misãlinsa tãre da shi, haƙĩƙa, dã sun yi fansa da shi. Waɗancan sunã da mummunan bincike kuma matabbatarsu Jahannama ce, kuma tir da ita ta zama shimfida.
( 1 ) Allah Mamallakin ruwa, Yanã kiran mutãne dõmin Ya bã su ruwan su shã. Su kuma kãfirai sunã kiran waɗansu abũbuwa dabam waɗandakõ karɓa musu kiran bã zã su iya yi ba, kuma sunã nẽman ruwa daga gare su, alhãli kuma ba su mallaki kõme ba. Watau Mai abu Yanã kiran su dõmin Ya bã su, sun ƙi karɓa Masa sai sunã kiran wani wanda bai mallaki kõme ba, sunã rõƙon Sa ruwa.
( 2 ) Idan ruwa ya sauka daga sama sa'an nan ya gudãna a cikin rãfuna zai yi kumfa. Sai ruwa mai amfãnin mutãne ya nutse a ƙasa ya zauna, sa'an nan kumfan kuma ya ƙẽƙashe ya lãlãce. Haka kuma idan an sanya ƙarfe na zinãri kõ na azurfa kõ baƙin ƙarfe a cikin wuta, aka zuga ta a kansa, zai fitar da kumfa, wãtau tsakin tama wanda zã a fitar dõmin rashin amfãninsa, dõmin zĩnariyar ƙwarai mai amfãni ta wanzu. To haka ga kõme akwai kumfa marashin amfãni da mai kyãwo mai amfani.
( 3 ) Bãyan da ya faɗi cẽwa Allah Yanã kira, kiran gaskiya a cikin ãyã ta l4, kuma waɗansu mutãne sun ƙi karɓar kiran Allah, sai sunã kiran waɗansu abũbuwa dabam, sai ya bayyana, a nan, sakamakon wanda ya karɓi kiran Allah sãmun ruwan sha, sabõda Mai abu ne Ya kirãwo shi, Ya kuma bã shi, ya sha a hankali kwance, sa'an nan kuma Allah zai bã shi abin da ya fi ruwan kyau, watau Aljanna. Amma wanda ya ƙi karɓãwa, to, yã yi hasãra biyu, bai sãmi ruwan da ya yi kiran wani ya bã shi ba, sa'an nan kuma ya haɗu da azãbar da take zai iya bãyar da dukan abin da ya mal1aka dõmin ya yi fansar kansa da ita.