Hausa translation of the meaning Page No 517

Quran in Hausa Language - Page no 517 517

Suratul Al-Hujurat from 12 to 18


12. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku nĩsanci abu mai yãwa na zato. Lalle sãshen zato laifi ne. Kuma kada ku yi rahõto, kuma kada sãshenku yã yi gulmar sãshe. Shin, ɗayanku nã son yã ci naman ɗan'uwansa yanã matacce? To, kun ƙĩ shi ( cin nãman ) . Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Mai karɓar tũba ne, Mai jin ƙai.
13. Yã kũ mutãne! ( 1 ) Lalle ne Mũ, Mun halitta ku daga namiji da mace, kuma Muka sanya ku dangõgi da kabĩlõli, dõmin ku san jũna. Lalle mafĩfĩcinku daraja a wurin Allah, ( shĩ ne ) wanda yake mafĩfĩcinku a taƙawa. Lalle nẽ Allah Masani ne, Mai ƙididdigẽwa.
14. Ƙauyãwa suka ce: « Mun yi ĩmãni. » Ka ce: « Ba ku yi ĩmãni ba, amma dai ku ce, 'Mun mĩƙawuya, ĩmani bai gama shiga a cikinzukãtanku ba. Kuma idan kun yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, to, bã zai rage muku kõme daga ayyukanku ba. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. »
15. Mũminan gaskiya kawai, sũ ne waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da ManzonSa, sa'an nan ba su yi shakka ba, kuma suka yi jihãdi da dũkiyarsu da kuma rãyukansu, cikin tafarkin Allah. Waɗannan sũ ne mãsu gaskiya.
16. Ka ce: « Kuna sanar da Allah ne game da addininku, alhãli kuwa Allah Yã san abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa, kuma Allah Masani ne ga dukan kõme? »
17. Suna yin gõri a kanka wai sun musulunta. Ka ce: « Kada ku yi gõrin kun musulunta a kaina. Ã'a, Allah ne ke yi muku gõri dõmin Ya shiryar da ku ga ĩmãni, idan kun kasance mãsu gaskiya. »
18. « Lalle Allah yanã sanin gaibin sammai da Ƙasa, kuma Allah Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa. »
( 1 ) Yã kirãyi mãsu ĩmãni a cikin wannan sũra sau biyar ga abin da ya kẽɓanta da su na umurni da hani kamar yadda Lukmãn ya kirãyi ɗansa wajen yi masa wasiyyõyi. Kuma ya kirãyi mutãne a wannan ãyã ga abin da ya haɗa mũminai da kãfirai wajen halitta, watau alfahari da dangantaka. Dangantaka bã ta ɗaukaka wanda taƙawarsa ba ta ɗaukaka shi ba, kuma bã ta rage wanda taƙawarsa ta ɗaukaka shi. Fĩfĩkon taƙawa, shĩ ne fĩfĩkotabbatacce.