Hausa translation of the meaning Page No 128

Quran in Hausa Language - Page no 128 128

Suratul Al-An'am from 1 to 8


Sũratul An‘ãm
Tanã karantar da tauhĩdi da tsarkake aƙĩda da ayyuka daga al’ãdu na shirki da kãfirci. Babu mai yanka hukunci a kan kõme sai Allah kawai, watau Tauhĩdin Rubũbiyya ke nan.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya halitta sammai da ƙasa, kuma Ya sanya duffai da haske ( 1 ) , sa'an nan kuma waɗanda suka kãfirta, da Ubangijinsu suke karkacewa.
2. Shi ne wanda Ya halitta ku daga lãkã, sa'an nan kuma Ya yanka ajali alhãli wani ajali ambatacce yanã wurinSa. Sa'an nan kuma ku kunã yin shakka.
3. Kuma Shĩ ne Allah a cikin sammai, kuma a cikin ƙasa Yanã sanin asĩrinku da bayyanenku, kuma Yanã sanin abin da kuke yi na tsirfa.
4. Kuma wata ãyã daga Ubangijinsu ba zã ta jẽ musu ba, fãce su kasance, daga gare ta, mãsu bijirẽwa.
5. Sabõda haka, lalle sun ƙaryata ( Manzo ) game da gaskiya, a lõkacin da ta jẽ musu, to lãbãrun abin da suka kasance sunã izgili da shi, zã su jẽ musu.
6. Shin, ba su gani ba, da yawa Muka halakar da wani ƙarni daga gabãninsu, Mun mallaka musu, a ckikin ƙasa, abin da ba Mu mallaka muku ba kuma Muka saki sama a kansu tanã ta zuba, kuma Muka sanya kõguna sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sa'an nan Muka halakã su sabõda zunubansu kuma Muka ƙãga halittar wani ƙarni na dabam daga bayansu?
7. Kuma dã Mun sassaukar da wani littãfi, zuwa gare ka, a cikin takarda, sa'an nan suka taɓa shi da hannuwansu, lalle dã waɗanda suka kãfirta sun ce: « Wannan bai zama ba, face sihiri bayyananne. »
8. Suka ce: « Don me ba a saukar da wani malã'ika ba a gare shi? » to dã Mun saukar da malã'ika haƙĩƙa dã an hukunta al'amarin ( 2 ) sa'an nan kuma ba zã a yi musu jinkiri ba.
( 1 ) Duffai na dare da zãlunci dabin hukunce- hukuncen al'ãdu, haske kuma shĩ ne na taurãri da wuta da shari'u na Littãfi da annabci.
( 2 ) Dã an hukunta al'amari da halakarsu, dõmin idan malã'ika ya sauka ga mutãnen da ake yi wa wa'azi bayyane, to, halakarsu tã je ke nan.