Hausa translation of the meaning Page No 283

Quran in Hausa Language - Page no 283 283

Suratul Al-Asra from 8 to 17


8. Akwai tsammãnin Ubangijinku Ya yi muku rahama. Kuma idan kun sãke Mu sãke. Kuma Mun sanya Jahannama matsara ga kãfirai.
9. Lalle ne wannan Alƙur'ãni yanã shiryarwa ga ( hãlayen ) waɗanda suke mafi daidaita ( 1 ) kuma yanã bãyar da bushãra ga mũminai waɗanda suke aikata ayyuka na ƙwarai ( cẽwa ) « Lalle ne sunã da wata ijãra. mai girma. »
10. Kuma lalle ne, waɗanda ba su yin ĩmãni da Lãhira, Mun yimusu tattalin wata azãba mai raɗaɗi.
11. Kuma mutum yanã ( 2 ) yin addu'a da sharri kamar addu'arsa da alhẽri, kuma mutum ya kasance mai gaggãwa.
12. Kuma Mun sanya dare da rãna, ãyõyi biyu, sa'an nan Muka shãfe ãyar dare, kuma Muka sanya ãyar rãna mai sanyãwa a yi gani, dõmin ku nẽmi falala daga Ubangijinku, kuma dõmin ku san ƙidãyar shẽkara da lissafi. Kuma dukan kõme Mun bayyana shi daki- dakin bayyanãwa.
13. Kuma kõwane mutum Mun lazimta masa abin rekõdinsa a cikin wuyansa, kuma Mu fitar masa a Rãnar Ƙiyãma da littãfi wanda zai haɗu da shi buɗaɗɗe.
14. « Karanta Littãfinka. Ranka ya isa ya zama mai hisãbi a kanka a yau. »
15. Wanda ya nẽmi shiryuwa, to, ya nẽmi shiryuwa ne dõminkansa kawai kuma wanda ya ɓace, to, ya ɓace ne a kansa kawai kuma rai mai ɗaukar nauyi bã ya ɗaukar nauyin wani ran, kuma ba Mu zama mãsu yin azãba ba, sai Mun aika wani Manzo.
16. Kuma idan Mun yi nufin Mu halakar da wata alƙarya, sai Mu umurci mawadãtanta, har su yi fãsicci a cikinta, sa'an nan maganar azãba ta wajaba a kanta, sa'an nan Mu darkãke ta, darkãkẽwa.
17. Kuma da yawa Muka halakar da al'ummomi a bãyan Nũhu. Kuma Ubangijinka Ya isa ya zama Mai ƙididdigewa ga zunubban bãyinSa, Mai gani.
( 1 ) Bãyan ya faɗi abũbuwan da Attaura ta karantar, ya ce: « Alƙur'ãni yanã shiryarwa zuwa ga hãlãyen da suka fi daidaita daga abin da Attaura ta karantar. » Sa'an nan ya ci gaba da bayãnin abũbuwan da Alƙur'ãni yake karantarwa.
( 2 ) Alƙur'ani yanã shiryar da mutum har ga yadda yake yin addu'a dõmin kada ya yi wa kansa addu'a ta sharri alhãli kuwa yanã nufin ya yi alhẽri dõmin an halicci mutum da son gaggãwa.