Hausa translation of the meaning Page No 595

Quran in Hausa Language - Page no 595 595

Suratul Al-Shams from 1 to 14


Sũratush Shams
Tana karantar da cewa idan azãba ta Sauka a kan mutãne takan shãfi mai laifi da wanda bã shi da laifi daga cikinsu.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Ina rantsuwa da rãnã da hantsinta.
2. Kuma da wata idan ya bi ta.
3. Da yini a lõkacin da ya bayyana ta.
4. Da dare a lõkacin da ya ke rufe ta.
5. Da sama da abin da ya gina ta.
6. Da ƙasã da abin da ya shimfiɗa ta.
7. Da rai da abin da ya daidaita shi.
8. Sa'an nan ya sanar da shi fãjircinsa da shiryuwarsa.
9. Lalle ne wanda ya tsarkake ( 1 ) shi ( rai ) ya sãmi babban rabo.
10. Kuma lalle ne wanda ya turbuɗe ( 2 ) shi ( da laifi ) ya tãɓe.
11. Samũdãwa sun ƙaryata ( Annabinsu ) , dõmin girman kansu.
12. A lõkacin da mafi shaƙãwarsu ya tafi ( wurin sõke rãkumar sãlihu ) .
13. Sai Manzon Allah ya gaya musu cewa: « Ina tsõratar da ku ga rãƙumar Allah da ruwan shanta! »
14. Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan suka sõke ta. Sabõda haka Ubangijinsu Ya darkãke su, sabõda zunubinsu. Sa'an nan Ya daidaita ta ( azãbar ga mai laifi da maras laifi ) .
15. Kuma bã ya tsõron ãƙibarta ( ita halakãwar ) .
Sũratul Lail
Tana karantar da dangantaka tsakanin ɗabi’a da halitta da ãƙibar mutum bisa aikinsa da kuma kasuwar abubuwa tsakanin alheri da sharri.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Inã rantsuwa da dare a lõkacin da yake rufẽwa.
2. Da yini a lõkacin da yake kuranyẽwa.
3. Da abin da ya halitta namiji da mace.
4. Lãlle ne ayyukanku, dabam- dabam suke.
5. To, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi taƙawa.
6. Kuma ya gaskata kalma ( 3 ) mai kyãwo.
7. To, zã Mu sauƙaƙe masa har ya kai ga sauƙi.
8. Kuma amma wanda ya yi rõwa, kuma ya wadãtu da kansa.
9. Kuma ya ƙaryatar da kalma mai kyãwo.
10. To, zã Mu sauƙaƙke masa har ya kai ga tsanani.
11. Kuma dũkiyarsa ba ta wadãtar masa da kõme ba, a lõkacin da ya gangara ( a wuta ) .
12. Lãlle aikinMu ne, Mu bayyana shiriya.
13. Kuma lalle ne Lãhira da duniya Namu ne.
14. Sabõda haka, Na yi maku gargaɗi da wuta mai babbaka.
( 1 ) Karɓar imãni da aiki da abinda ya ƙunsa tsarkake rai ne.
( 2 ) Kãfirci turbuɗe rai ne da zunubi.
( 3 ) Kalma mai kyãwo ita ce Kalmar shahãda da abin da ta ƙunsa na addinin Musulunci, wanda yake yinsa kamar yadda Allah Ya ce, ta hanyan ManzonSa, shi ne taƙawa.